Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; Za a fara gudanar da wani zaman taro dangane da yanayin rayuwar musulmi a kasashen da suke su ne marassa rinjaye da hakan ya hada da kasashen turai da kuma wasu kasashe na latin Amurka da wasu yankunan nahiyar Asia. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai yi dubi ne kan irin taimakon da ya kamata a rika bai wa musulmi a kasashen da suke su ne marassa rinjaye, daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a taimaka ma musulmin wadannan kasashe shi ne batun kafa wasu hanyoyi na karfafa su a ilmance da m ta fuskacin tattalin arziki ta yadda za su dogara da kansu.
425574