IQNA

OIC Ta Kirayi Kasashen Turai Da Su Canja Siyasarsu Dangane Da Musulunci

8:58 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795568
Bangaren kasa da kasa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihasan Oglu ya kirayi kasashen yammacin turai da su canja siyasarsu dangane da kasashen musulmi, ya kuma bayyana hakan ne a taron karawa juna ilimi na na shekara-shekara a birnin Bruksel na kasar Belgium.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancn labaran zaman cewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihasan Oglu ya kirayi kasashen yammacin turai da su canja siyasarsu dangane da kasashen musulmi, ya kuma bayyana hakan ne a taron karawa juna ilimi na na shekara-shekara a birnin Bruksel na kasar Belgium. Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen taron babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya bayyana cewa kasashen yammacin turai suna bin wani salo na siyasa na takura wa kasashen musulmi, wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da suke kara kawo baraka tsakanin kasashen musulmi da na turai, wanda kuma dole ne a kawo karshen wannan baraka da rashin jituwa.

425541



captcha