IQNA

An Fara Bayar Da Horo Kan Hardar Kur'ani A Birnin Qods

17:02 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795925
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani a birnin Qods mai alfarma, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta palastinu ta dauki nauyin shiryawa a cikin watannin Rajab da kuma sha'aban.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran PNN cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani a birnin Qods mai alfarma, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta palastinu ta dauki nauyin shiryawa a cikin watannin Rajab da kuma sha'aban. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wanna shiri ita ce karfafa gwiwar matasa wajen mikewa tsaye domin mayar da hankali ga karatun kur'ani da kuma hardarsa a dukkanin yankunan palastinawa, shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani a palastinu ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen shiryar da matasa zuwa ga kur'ani da koyarwarsa a yankin.

426051





captcha