Bangaren kasa da kasa; wasu daga cikin jam'iyun siyasar kasar Norway masu tsattsauran ra'ayi sun bullo da wani shiri na tsoratar da mutanen kasar, inda suke bayyana musu cewa bincike ya tabbatar da cewa daga nan zuwa shekara ta 2085 kasar Norway za ta zama kasar musulmi baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kabs cewa; wasu daga cikin jam'iyun siyasar kasar Norway masu tsattsauran ra'ayi sun bullo da wani shiri na tsoratar da mutanen kasar, inda suke bayyana musu cewa bincike ya tabbatar da cewa daga nan zuwa shekara ta 2085 kasar Norway za ta zama kasar musulmi baki daya. Daya daga cikin jam'iyun da suke da wannan manufa ita ce jam'iyar 'yan kasa, wadda day ace daga cikin manyan jamiyun kasar da ke da tsattsauran ra'ayin kiyayya da addinin musulunci, wanda kuma bababr manufar hakan ita ce tunzura al'ummar kasar Norway domin su fada kan musulmi wadanda su ne marassa rinjaye.
425954