Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na horar da mata hardar kur'ani mai tsarki a birnin Jidda na kasar saudiyya, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta kasar Saudiyya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na 47 online cewa; An fara gudanar da wani shiri na horar da mata hardar kur'ani mai tsarki a birnin Jidda na kasar saudiyya, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta kasar Saudiyya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani a birnin jidda, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta saudiyya ta dauki nauyin shiryawa a cikin watannin Rajab da kuma sha'aban. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wanna shiri ita ce karfafa gwiwar matasa wajen mikewa tsaye domin mayar da hankali ga karatun kur'ani da kuma hardarsa a dukkanin yankunan , shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen shiryar da matasa zuwa ga kur'ani da koyarwarsa a yankin.
425928