Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga wasu daga cikin musulmin kasar Birtaniya, dangane da yadda za su koyi kyawan dabi'u ga daidai da koyarwar addinin musulunci, bisa la'akari da yanayin wurin da suke rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ic el cewa; Za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga wasu daga cikin musulmin kasar Birtaniya, dangane da yadda za su koyi kyawan dabi'u ga daidai da koyarwar addinin musulunci, bisa la'akari da yanayin wurin da suke rayuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa al'ummar musulmi da suke rayuwa a kasashen yammacin turai wadanda su marassa rinjaye suna bukatar kafafa gwiwa daga sauran musulmi, ta hanyar ilmantarwa da kuma samara musu da wasu shirye –shirye na karfafa imaninsu da kuma kauce wa fadawa cikin gurbatar dabi'u, musamman ma matasa daga cikinsu, wadanda suke saurin kamuwa dab akin dabi'u.
425857