Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Qatar, wanda hukumar kula da harkokin addinin musulunci a kasar ta dauke nauyin gudanarwa a birnin Doha fadar mulkin kasar ta Qatar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran peninsula cewa; An gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Qatar, wanda hukumar kula da harkokin addinin musulunci a kasar ta dauke nauyin gudanarwa a birnin Doha fadar mulkin kasar ta Qatar. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da wannan gasar ne a bangarorin harda da karatu da kuma tajwidi, inda talibai mata makaranta kur'ani da kuma mahardata suka shiga ciki, an kuma bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka samu nasar lashe wannan gasar.
425732