IQNA

An Gudanar Da Bangaren Karshe Na Gasar Kiran Salla A Turkiya

17:04 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795984
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da bangaren karshe na gasar kiran salla a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa a birnin Yalova na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran saman cewa; An gudanar da bangaren karshe na gasar kiran salla a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa a birnin Yalova na kasar Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da wannan taro da ya kunshi gasar kiran salla na da matukar muhimmanci ga al'ummar musulmin kasar, domin kuwa hakan zai karfafa gwiwar musulmi wajen mayar da hankali ga addininsu musamman ma matasa daga cikinsu da ake yaudarar tunaninsu, inda ake bata al'adunsu tare da cusa musu tunanin turai.

425803
captcha