IQNA

Aljeriya Ce Za Ta Dauki Bakin Taron Komitin Zartarwa Na OCI A Karon Farko

Bangaren kasa da kasa: taron komitin zartarwa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na ashirin da daya za a gudanar da shi ne a kasar Aljeria.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga Elmoudjahid cewa wannan taro na kwanaki biyu da duniyar musulmi za ta hade wakilai da za su halarci gurin wannan taro za su fi maida hankali ne kan matsalolin da suka addabi al'ummar Palasdini da tunanin hanyoyin magance irin wadannan matsaloli da suka yi masu kanta da kuma yin dubi a cikin wasu matsalolin da suka shafi sauran kasashen musulmi da musulmi.

425750