IQNA

Fara Koyar da Mata Karatun Kur'ani A Mazarif Sharif

17:03 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795989
Bangaren da ke kula da harkokin kur'ani: A garin Mazari Sharif na kasar Afganistan an fara koyar da mata karatun kur'ani a daidai wannan lokaci na hutu.
Daga Afganistan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a garin mazaril Sharif a daidai wannan lokaci na fara hutun karshen shekarar karatu a makaratun garin ana koyar da mata karatun kur'ani da harda da kuma tajwidi a wani mataki na kara ilmantar da su sanin harkokin addinin musulunci musamman karatun kur'ani mai girma.

425723
captcha