Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran dunya bulteni cewa; Babbar jami'ar nan ta musulunci dake kasar Uganda daya ce daga cikin manyan jami'oin nahiyar Afirka da suke daukar dalibai kowace shekara tare da yaye su a kowace shekara. Bayanin ya ci gaba da cewa jami'ar musulunci ta kasar Uganda da aka kafa tat un shekara ta 1988, ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan musulumi musamman ma yankunan da ke gabacin nahiyar Afirka, jami'ar ta fara da dalibai 80 amma daga bisani ta samu gagarumar karbuwa daga musulmi da ma wadanda ba musulmi, lamarin da ya kai jami'ar a halin yanzu tana da dubban dalibai, inda takan dauki daruruwan dalibai a sassa daban-daban na ilimi a kowace shekara, haka nan kuma tana yayewa.
426517