IQNA

Za A Gyara Masallatan Kasar Gabanin Watan Ramadan

16:42 - June 29, 2009
Lambar Labari: 1796394
Bangaren kasa da kasa; Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Qatar ta sanar cewa; za a gyara masallatan kasar katar ga baki daya, a lokacin da watan azumin Ramadan ke karatowa, inda yanzu haka kimanin masallatai 40 aka shirya gudanar da gyare-gyare a cikinsu domin tarabar watan azumi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran peninsula cewa; Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Qatar ta sanar cewa; za a gyara masallatan kasar katar ga baki daya, a lokacin da watan azumin Ramadan ke karatowa, inda yanzu haka kimanin masallatai 40 aka shirya gudanar da gyare-gyare a cikinsu domin tarabar watan azumi. Daya cikin m,anyan daraktocin ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Qatar ya bayyana cewa, yanzu haka dai kimanin masallatai 1200 a fadin kasar katar, kuma tuni ma'aikatar ta hada rahotanni dangane da yanayin da masallatan suke ciki, domin duba masallatan da suke bukatar gyara, inda masallatai arba'in ne daga ciknsu ke bukatar gyare-gyare, kuma za a kamamla gyaransu daga nan ziuwa kafin fara azumi.


426411




captcha