Bangaren kasa da kasa; Bangaren kula da harkoki da nazari kan ddinin musulunci na jami'ar Starbourg na kasar Faransa, ya fara guga wata mujalla da take fayyace mahangar muslunci dangane da harkokin tattalin arziki, kuma bad a jimawa ba za a fara yada ta a matsayi na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na e-tud.com cewa; Bangaren kula da harkoki da nazari kan ddinin musulunci na jami'ar Starbourg na kasar Faransa, ya fara guga wata mujalla da take fayyace mahangar muslunci dangane da harkokin tattalin arziki, kuma bad a jimawa ba za a fara yada ta a matsayi na kasa da kasa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan bangare na taka rawa wajen wayar da kan masu bincike kan harkokin tattalin arziki da kuma bayyana musu mahangar musulunci kan harkokin tattalin arziki, wanda kuma masana daga jami'oin musulunci suke bayar da gudunmawarsu wajen rubuta makaloli a cikin wannan mujallar.
426449