IQNA

Za A Fara Gudanar Da Wani Shiri Na Horar Matasa Kan Karatun Kur'ani

16:40 - June 29, 2009
Lambar Labari: 1796399
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani shiri na horar da matasa kan karatun kur'ani da harda, wanda kwamitin kula da harkokin ilimin addinin addinin musulunci a kasar, wanda za a gudanar a birnin Wujdah, da nufin karfafa gwiwar matasa wajen mayar da hankali kan harkokin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran city.net cewa; Za a fara gudanar da wani shiri na horar da matasa kan karatun kur'ani da harda, wanda kwamitin kula da harkokin ilimin addinin addinin musulunci a kasar, wanda za a gudanar a birnin Wujdah, da nufin karfafa gwiwar matasa wajen mayar da hankali kan harkokin kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hanakali kansu akwai karatun kur'ani da kuma hardarsa, gami da wasu ilmomi na addinin musulunci, kama daga ilmin fikihu da kuma tajwidi, da kuma balaga gami da littafan hadisi. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kwamitin zai kara mayar da himma wajen aiwatar wannan shekara.

426413



captcha