IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar La'antar Shimon Peres A Turkiya

16:57 - June 30, 2009
Lambar Labari: 1796978
Bangaren kasa da kasa; Dubban mutanen kasar Turkiya ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Istanbul fadar mulkin kasar a jiya, domin la'antar shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila Shimon peres da yake kai ziyara a kasar Azarbaijan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran velfecr cewa; Dubban mutanen kasar Turkiya ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Istanbul fadar mulkin kasar a jiya, domin la'antar shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila Shimon peres da yake kai ziyara a kasar Azarbaijan. Masu gudanar da zanga-zangar sun daga tutocin kungiyoyin gwagwarmaya na Hamas da hizbullah, da hotunan wasu daga cikin wadanda suka yi shahada a hare-haren ta'addancin da sojojin Isra'ola suka kai akn al'ummomin labanan da palastinu. Sun gudanar da zanga-zangar ne a gaban ofishin jakadancin kasar Azarbaijan da ke birnin Istanbul.

427071



captcha