IQNA

An Yi Allawadai Da Hana Ginin Hasumiyar Masallaci A Switzerland

16:56 - June 30, 2009
Lambar Labari: 1796980
Bangaren kasa da kasa; Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa emnesty international ta yi Allawadai da matakin da jam'iyun siyasar kasar Swedeen masu tsattsauran ra'yin kiyayya da musulunci suka dauka na hana gina hasumiyar masallaci kasar, hukumar ta ce wannan mataki ne na tsokanar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa emnesty international ta yi Allawadai da matakin da jam'iyun siyasar kasar Swedeen masu tsattsauran ra'yin kiyayya da musulunci suka dauka na hana gina hasumiyar masallaci kasar, hukumar ta ce wannan mataki ne na tsokanar musulmi. Shugaban ofishin hukumar kare hakkin bil adama da ta kasa da kasa da ke kasar Switzerland shi ne ya sanar da hakan a cikin wani bayani da ya fitar jiya, ya ci gaba da cewa wannan mataki ba shi da wata dangantaka da abin da wadanna jam'iyu suke bayyanawa, illa dai kawai tsananin gab ace da ake nuna wa musulmi marassa rinjaye da ke kasar.

427103




captcha