Bangaren kasa da kasa; Kasashen yammacin turai suna ci gaba da nuna goyon baya na ido rufe ga siyasar zalunci da danniya da kisan gilla da Isra'ila ta ke yi kan al'ummar palastinu marassa kariya, a lokaci guda kuma suna zargin kasashen musulmi da marawa ayyukan ta'addanci baya, wannan shi ne sirrin adawar musulmi da siyasar yammacin turai.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na nasij cewa; minister mai kula da harkokin addinin musulunci na kasar Masar Mahmud Hamdi ya bayyana cewa; Kasashen yammacin turai suna ci gaba da nuna goyon baya na ido rufe ga siyasar zalunci da danniya da kisan gilla da Isra'ila ta ke yi kan al'ummar palastinu marassa kariya, a lokaci guda kuma suna zargin kasashen musulmi da marawa ayyukan ta'addanci baya, wannan shi ne sirrin adawar musulmi da siyasar yammacin turai. Ya ci gaba da cewa musulmi suna ji a jikinsu cewa kasashen yammacin turai bas u dawata niyya ta alhairi dangane da musulmi saboda abin da suke gani a zahiri na zalunci da nuna rashin gaskiya.
427057