Bangaren kasa da kasa; An bude wani shafin internet a birnin Riyad na kasar Saudiyya da nufin harhada bayanai da labarai da suka danganci ayyuka da harkokin addinin musulunci da al'adun musulmi da kuma harkoki da suka danganci kur'ani musamman, wanda cibiyar kula da aharkokin addini ta sarki fahad ta dauki nauyin gatarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Saudiyya ta Riyad cewa; An bude wani shafin internet a birnin Riyad na kasar Saudiyya da nufin harhada bayanai da labarai da suka danganci ayyuka da harkokin addinin musulunci da al'adun musulmi da kuma harkoki da suka danganci kur'ani musamman, wanda cibiyar kula da aharkokin addini ta sarki fahad ta dauki nauyin gatarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wanna shafin internet zai mayar da hankali wajen yada al'amurra da suka shafi addinin musulunci, tare da mayar da martani kan shubhohin da ake yi kana addinin musulunci, domin kuwa daga cikin dalilan bude wannan shafi har da isar da sakon addinin musulunci ga wadan dab a musulmi ba, domin sanin irin koyarawar addini da kuma bayyana musu hakikanin abin da ke tattare da wannan addinin sabanin abin da makiya musulunci suke nunawa a shafukan internet.
427009