Bangaren kasa da kasa; A jiya ne a ka gudanar da bikin girmama mahardaci kuma makarancin kur'anin na kasar Yeman Sheikh Yasin Bin Ahmad yasin a birnin Hadra maut na kasar Yeman, wanda ya shahara dad a karatun kur'ani da nau'oin kira har goma, daga cikin kira'oin da aka sani a musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikkna ya nakalto daga shafin internet na Yeman news cewa; A jiya ne a ka gudanar da bikin girmama mahardaci kuma makarancin kur'anin na kasar Yeman Sheikh Yasin Bin Ahmad yasin a birnin Hadra maut na kasar Yeman, wanda ya shahara dad a karatun kur'ani da nau'oin kira har goma, daga cikin kira'oin da aka sani a musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa sheikh yasin bin Ahmad yasin daya daga cikin makaranta kur'ani da suka shahara a duniya, domin kuwa salon karatun da yake amfani da shi salon e wanda ya sha banban da sauran masu karatu, a lokaci guda dai akwai kyautata karatun kamar yadda ya kamata, sa'anna kuma ga ilmantarwa, domin kuwa yana kawo kira'oi daban-daban a cikin karatunsa.
426987