Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, wadda ta hada bangarorin harda da kuma karatu gami da tafsiri da tajwidi, haka nan kuma ta hada bangaren maza da kuma bangaren mata, wadda aka kammala a bin Manama fadar mulkin kasar Bahrain.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Bahrain cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, wadda ta hada bangarorin harda da kuma karatu gami da tafsiri da tajwidi, haka nan kuma ta hada bangaren maza da kuma bangaren mata, wadda aka kammala a bin Manama fadar mulkin kasar Bahrain. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ce ta dauki nauyin shirya tare da gudanar da gasar, tare da hadin gwiwar cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani ta kasar. An bayar da kyaututuka ga wadanda suka samu zuwa a mataki na farko da kuma na biyu gami d na uku a cikin kowane rukuni.
426956