IQNA

An Yi Suka Kan Yin Afani Da Hadisai Wajen Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi

Bangaren fikira da ilimi; Cibiyar kula da harkokin ilimin hadisi ta darul hadis ta karya lagon masu yin amfani da hasan manzon Allah wajen kawo rarraba tsakanin mabiya addinin musulunci, domin cimma wasu manufofi da za su amfani makiya musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar kula da harkokin limin hadisi cewa; Cibiyar kula da harkokin ilimin hadisi ta darul hadis ta karya lagon masu yin amfani da hasan manzon Allah wajen kawo rarraba tsakanin mabiya addinin musulunci, domin cimma wasu manufofi da za su amfani makiya musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga cikin malaman ilimin hadisi a cibiyar kula da nazari kan ilmomin hadisi a kasar Sudan Ali Muhammad ya bayyana cewa; abin ban takaici ne yadda wasu daga malaman addinin musulunci a wasu kasashe suke amfani da hadisan manzon Allah wajen kawo rarraba a tsakanin mabiya addinin musulunci, ya ce dole a dauki dukkanin matakan da suka dace domin kawo karshen wannan matsala.

427510