IQNA

Za A Guadanar Da Gasar Kur'ani Ta Nakasassu A UAE

15:28 - July 01, 2009
3
Lambar Labari: 1797345
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar harda da karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci nakasassu a kasar hadaddiyar daular larabawa, a birnin sharjah, wanda cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar suka dauki nauyin shiyawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam cewa; Za a gudanar da gasar harda da karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci nakasassu a kasar hadaddiyar daular larabawa, a birnin sharjah, wanda cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar suka dauki nauyin shiyawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa abbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce kara karfafa gwiwar nakasassu da ke fadin kasar wajen mayar da hankali ga karatu da harder kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa abban kuskuren da ake yi a cikin al'umma shi ne yadda ake mayar da nakassu saniyar ware a cikin mafi yawan harkokin, amma saka su zai taimaka wajen su ji cewa suma wani bangare ne na al'umma.

427545


Wanda Aka Watsa: 3
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Abba Hamza
0
0
Haka zai kara karfafa mana gwaiwa wajen kara haddace alkur ani
Abba Hamza
0
0
Haka zai kara karfafa mana gwaiwa wajen kara haddace alkur ani
Abba Hamza
0
0
Haka zai kara karfafa mana gwaiwa wajen kara haddace alkur ani
captcha