IQNA

Hana Saka Hijabin Musulunci Ya Yi Hannun Riga Da Kare Hakkin Bil Adama

Bangaren rahoto; Wani masani kan harkokin shai'a da kare hakkin bil adama na kasar Iran Ruhullah Ramazan Pour Karimi ya bayyana cewa; tilasta mata musulmi da su daina saka hijabin musulunci ya yi hannu riga da duk wasu hakkoki na bil adama, kuma hakan ba ya cikin dabi'un masu kare hakkin dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na human rights.net cewa; Wani masani kan harkokin shai'a da kare hakkin bil adama na kasar Iran Ruhullah Ramazan Pour Karimi ya bayyana cewa; tilasta mata musulmi da su daina saka hijabin musulunci ya yi hannu riga da duk wasu hakkoki na bil adama, kuma hakan ba ya cikin dabi'un masu kare hakkin dan adam. Masanin ya ci gaba da cewa bisa hujjar cewa su babu ruwansu da addini akan haka ba za su bari mata musulmi su saka hijabi ba, ya ce amma a lokaci guda suna ikirari cewa suna kare hakkokin dan adam, ya ce ina batun kare hakkin dan a cikin hana saka hijabi, bil hasali ma hakan danne hakkokin dan adam ne, domin dan adam yana hakkin ya saka tufafin da suka dace domin suturta jikinsa, babu wata doka da ta hana hakan ko a kasashensu.

427507