Bangaren al'adu da fasaha; An tarjama littafin nan na nahjul fasaha zuwa yaren mutanen kasar Chana, wanda bangaren kula da harkokin ilmi da al'adu na kasar Iran ya dauki nauyin fassarawa, kuma cibiyar chiyan ji ta kasar Chana ta dauki nauyin bugawa da yadawa a fadin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An tarjama littafin nan na nahjul fasaha zuwa yaren mutanen kasar Chana, wanda bangaren kula da harkokin ilmi da al'adu na kasar Iran ya dauki nauyin fassarawa, kuma cibiyar chiyan ji ta kasar Chana ta dauki nauyin bugawa da yadawa a fadin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafin yana dauke da gajerun hadisai na manzon Allah SAW, wanda kuma ko shakka babu hadisai ne da suke da matukar muhimmanci musulmi ya sansu domin gyara rayuwarsa ta zamantakewa, wanda hakan ke nufin cewa, ba wai kawai musulmi ba har ma sauran mabiya wasu addinai na daban za su iya yin amfani da abin da ke cikin littafin domin amfanuwar kansu.
427563