Bangaren siyasa da zamantakewa; Za a kafa wata babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a kasar Afganistan, wadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta za ta dauki nauyin kafawa domin ilmantar da al'ummomin wasu yankuna na kasar Afganistan kan muhimman da ya kamata na addinin musulunci, musamman ma mazauna karkara daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar hadin kasashen musulmi cewa; Za a kafa wata babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a kasar Afganistan, wadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta za ta dauki nauyin kafawa domin ilmantar da al'ummomin wasu yankuna na kasar Afganistan kan muhimman da ya kamata na addinin musulunci, musamman ma mazauna karkara daga cikinsu. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin ilmi da kuma tarbiya ta kasar, inda za a kafa cibiyar a lardin kapisa. Yanzu haka dai an fara gudanar da ayyuka na neman taimakon al'ummar kasar domin gina wannan cibiya.
427321