IQNA

Tsohon Shugaban Amurka Bush Ya Shahara Da Gaba Da Addinin Musulunci

15:29 - July 01, 2009
Lambar Labari: 1797353
Bangaren kasa da kasa; Tsohon shugaban kasar amurka G.W. Bush ya kama tafarki nuna kiyayya da gaba da addinin musulunci a lokacin mulkinsa, wanda hakanne ya jawo Amurka da dama daga cikin matsalolin da take fuskanta musamman aduniyar musulmi, inda Amurkawa su suke shan kunya dangane da aika-aikarsa a yanzu.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na muhit cewa; wani ma'aikacin gidan talabijin din kasar Amurka wanda bayahuden kasar ne zakub Bander, ya bayyana cewa; Tsohon shugaban kasar amurka G.W. Bush ya kama tafarki nuna kiyayya da gaba da addinin musulunci a lokacin mulkinsa, wanda hakanne ya jawo Amurka da dama daga cikin matsalolin da take fuskanta musamman aduniyar musulmi, inda Amurkawa su suke shan kunya dangane da aika-aikarsa a yanzu. Ya ci gaba da cewa ko alama abin da Bush ya yin a nuna tsananin gaba da addinin musulunci bai kyauta ba, kuma shi a halin yanzu yana jin kunyar musulmi, ya kara da cewa bin tafarki irin na Bush zai kai ga Amurka da Amurkawa zuwa ga halaka ne.

427585


captcha