IQNA

Yan Majalisar Dokoki A Kasashen Musulmi Sun Yi Allah Wadai Da Matakin HKI Kan Palasdinu

16:19 - July 01, 2009
Lambar Labari: 1797479
Bangaren kasa da kasa: Wakilai day an majalisar dokoki daga kasashen musulmi sun yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke dauka kan al'ummar Palasdinu.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta joyo kafar labarai ta Kuna a kasar Koweiti na cewa: komitin zartar na hadin guiwar majalisun dokoki a kasashen musulmi ya yi Allah wadai da mummunan mataki na dabbanci da gwamnatin yahudawan sahayoni ke dauka kan al'ummar musulmi ta Plasdinu tun kafin yaki da lokacin yaki da kuma bayan yaki na killacewa da baker azzaba da zalumci na karshe da suke nuna masu ba dare ba rana.

427607
captcha