IQNA

Kur'ani Shi Ne Mai Bayyana Hanya Ta Gaskiya Da Adalci

13:22 - July 02, 2009
Lambar Labari: 1797652
Bangaren harkokin kur'ani : Daya dayar hanyar tsirar da dan adam da kaucewa munanan siffofi da kama hanyar gaskiya da adalci ita ce riko da kur'ani mai tsarki.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Said Muhammad Husein Ra'is Zade shugaban ofishin yada al'adun Iran a London a cikin wani jawabi da ya gabatar a lokacin da ake rarraba kyautukan kammala gasar karatun kur'ani a makarantar Shahid a birnin Beirut ya bayyana cewa; a yau duniyar dan adam tana cike da munanan siffofi kamar girman kai,hasada,kashi,kwadayi.Amma kubuta daga ire-iren wadannan siffofi sai an rungumi fiyayyan littafi madaidaici wato Alkur'ani mai girma hanya ta gaskiya da adalci.

428176

captcha