IQNA

Wani Mai Bincike Kan Fatawar Kafirta Musulmi Yan Shiya Ya Ce Kuskure Ne

Bangaren manema labarai:daya daga cikin mai nazari da bincike bayan ya ziyarci Markadin Imam Huseini (AS) ya bayyana cewa; kafirta yan shi'a da fitar da fatawa kan haka babban kuskure ne.
Daga birnin Qum ne cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; Dokta Said Muhamad Tidjani Samawi wani mai bincike masali kan addinin musulunci ya bayyana cewa: duk da mummunan halin tsaro da tabarbarewarsa a Iraki na yi sa'ar ziyartar markadin Imam Huseini (AS) da na Imam Ali (AS) .Kuma fatawar da wasu malummai ke fitarwa na kafirta yan shi'a wani babban kuskure ne kuma ba a san abin da ya dace bad a maslahar musulmi kuma fitar da irin wannan fatawa wani aiki ne ga makiyan musulunci da kawo sabani a tsakanin musulmi.

428226