Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na UG cewa; An bude wata jami'ar musulunci a birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda, da nufin karfafa harkokin addinin musulunci ta fuskar ilimi da kuma a'adu. Bayanin ya ci gaba da cewa bude wannan jami'a na daya daga cikin shirye-shiryaen bangaren kula da harkokin addini na kwamitin yada addinin musulunci da ked a cibiya a birnin Tripoli na kasar Libya, Babban daraktan ma'aikatar ilimi ta kasar Uganda ya bayyana cewa babban ci gaba bude jami'oi irin wadannan da za su taimaka ma al'ummar kasar wajen kara samun masaniya dangane da addinin musulunci.
427944