Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Kimanin mutane 1763 ne suka musulunta a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin watannin farko na wannan shekara. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban bangaren da ke kula da lamurran musuluntar mutane a ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar hadaddiyar daular larabawa Huda Khalfan Ka'abi shi ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya bayyana cewa yanzu haka suna jerin sunayen mutanen da suka musulunta tun daga farkon shekarar nan a Dubai, wadanda dukkaninsu 'yan kasashen waje ne da suke zaune a kasar kom asuka zo domin gudanar da harkokin kasuwancinsu, saboda kyawan dabi'un da suka gani daga musulunci.
428256