IQNA

An Gudanar Da Gasar Kiran Salla A Birnin Batman Na Turkiya

23:32 - July 03, 2009
Lambar Labari: 1797695
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wata gasa ta kiran salla a birnin Batman na kasar Turkiya, wadda ta kebanci masu kula da harkokin masallatai da kuma cibiyoyin addinin musulunci da ke kasar, da nufin samar da ladanai masu kyawun sauti wajen kiran salla a masallatan da ke cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran el-aziz cewa; An gudanar da wata gasa ta kiran salla a birnin Batman na kasar Turkiya, wadda ta kebanci masu kula da harkokin masallatai da kuma cibiyoyin addinin musulunci da ke kasar, da nufin samar da ladanai masu kyawun sauti wajen kiran salla a masallatan da ke cikin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dai ba shi ne karon farko da aka gudanar da gasar kiran salla a kasar Turkiya ba, domin kuwa ko alokutan baya an gudanar da gasar kur'ani a sassa daban-daban na lardin Anatoli da ma sauran yankunan da keg abaci da kudancin kasar. A wannan karon an bayar da kyaututuka ga wadanda suka zo a matsayi na farko ko na biyu da na uku a cikin gasar.


428277

captcha