Bangaren kasa da kasa; An Kammala Gyaran Masallacin Mostafa Pahsa da ke birnin Scopia na kasar Makdonia, wanda hukumar kula da bunkasa kasa ta Turkiya ta dauki nauyin gyaransa, kuma za a bude shi a farkon watan Ramadan mai zuwa domin gudanar da harkokin musulunci a cikin wannan wata mai albarka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran haber cewa;
An Kammala Gyaran Masallacin Mostafa Pahsa da ke birnin Scopia na kasar Makdonia, wanda hukumar kula da bunkasa kasa ta Turkiya ta dauki nauyin gyaransa, kuma za a bude shi a farkon watan Ramadan mai zuwa domin gudanar da harkokin musulunci a cikin wannan wata mai albarka. An gina masallacin ne a cikin shekara ta 1949, kuma an fara gyaran shi net un a cikin shekara ta 2006. Masallacin na da matukar muhimmanci ga al'ummar musulmin kasar Makdodia, domin kuwa shi ne masallaci mafi girma a kasar, wanda kan hada dukkanin musulmi a lokacin da ake gudanar da wasu taruka a kasar da suka dangancin musulunci.
428314