Bangaren kur'ani; An gudanar da taron girmama wasu mahardata kur'ani mai tsarki na kasar Afganistan, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta Darulhifaz ta kasar Afganistan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Jabal siraj na kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Afganistan ya habarta cewa; An gudanar da taron girmama wasu mahardata kur'ani mai tsarki na kasar Afganistan, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta Darulhifaz ta kasar Afganistan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Jabal siraj na kasar Afganistan. Daya daga cikin malamai kuma dan siyasa da shahara a kasar Afganistan musamman ma lokacin yaki, Burhanuddini Rabbani, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa bai kamata a yi ta bayani kan muhimmancin karatun kur'ani ko hardarsa ko gudanar da gasarsa ba kawai ba tare da aikata a bin da ke cikinsa. Ya kara da cewa kur'ani mai tsarki ba yana bukatar karantawa ban e kawai, a a hakan na bukatar aiki lokaci guda.
429516