Bangaren siyasa da zamantakewa; A daidai lokacin da ake gabatar da shirye-shiryen bukukuwan maulidin Imam Ali (AS) a ranakun 13 ga watan Rajab, mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan ya bayyana cewa, sanin rayuwar Imam Ali (AS) na bukatar bincike tsantsa ba tare da nuna bangaranci ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; A daidai lokacin da ake gabatar da shirye-shiryen bukukuwan maulidin Imam Ali (AS) a ranakun 13 ga watan Rajab, mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan ya bayyana cewa, sanin rayuwar Imam Ali (AS) na bukatar bincike tsantsa ba tare da nuna bangaranci ba. Bayanin ya ci gaba da cewa Ayatollah Kabalan ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da akhlaq da ya saba gabatarwa a koda yaushe, inda ya bayyan acewa Imam Ali (AS) rayuwarsa ta danganci dukkanin bangarorin rayuwa ne na bil adam, domin ya bayar da misali da za a koyi da shi, kamar yadda rayuwar manzon Allah (SAW) ta kasance rayuwa ce da ke tattare da darussa gad an adam, kuma idan aka yi la'akari da rayuwar Imam ci gaban sakon da ke tattare da rayuwar manzon Allah ne.
429883