Bangaren siyasa da zamantakewa; Daya daga cikin manyan malaman kasar Iran Ayatollah Mukarim Shirazi a cikin wani bayani day a fitar zuwa ga masu gudanar da ibadar Itikafi ya bayyana cewa; ka da ku hada jin dadin munajati da ubangiji da wani abu na daban, ku shagaltu da ayyuka na tsarkake ruhi da kara imani da ikhlasi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen birnin Qom ya habarta cewa; Daya daga cikin manyan malaman kasar Iran Ayatollah Mukarim Shirazi a cikin wani bayani day a fitar zuwa ga masu gudanar da ibadar Itikafi ya bayyana cewa; ka da ku hada jin dadin munajati da ubangiji da wani abu na daban, ku shagaltu da ayyuka na tsarkake ruhi da kara imani da ikhlasi. Bayanin ya ci gaba da cewa, a cikin bayanin da shehin malamin ya aike wa msu ibadar ya kara da cewa, gudanar da irin aikin ibada yana da nasa matukar muhimmancin ta fuskoki da dama, da hakan ya hada da tsarkake ruhi da kuma tarbiyantar da shi wajen ayyukan ibada da biyayya ga Allah madaukakin sarki.
429877