Bangaren fikira da ilimi; Ana shirin gudanar da babban taro na kasa da kasa dangane da Salma Farisi a birnin Tehran, da nufin yin bahasi kan rayuwarsa da wulayarsa da kuma muhimman abubuwan day a kamata a koya daga rayuwarsa na bincike da neman gaskiya da kuma binta a duk inda aka sameta, da kuma biyayyarsa ga iyalan gidan manzon Allah SAW.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Ana shirin gudanar da babban taro na kasa da kasa dangane da Salma Farisi a birnin Tehran, da nufin yin bahasi kan rayuwarsa da wulayarsa da kuma muhimman abubuwan day a kamata a koya daga rayuwarsa na bincike da neman gaskiya da kuma binta a duk inda aka sameta, da kuma biyayyarsa ga iyalan gidan manzon Allah SAW. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo farko da za a gudanar da wani babban taro makamancin haka dangane da rayuwar Salman Farisi, taron zai samu halartar manyan baki daga kasashen musulmi da za su gabatar da laccoci tare da gabatar da makalolinsu kan rayuwar wannan sahabin manzon Allah. Haka nan kuma taron zai samu halartar baki na cikin gida da suka hada dam asana da malaman jami'a da dai sauransu.
429846