Bangaren al'adu da fasaha; Shugaban musulmin yankin kafkaz ya bayyana cewa; yaduwar murar aladu ba zai hana al'ummar musulmi na kasar Azarbaijan yin tafiya zuwa kasar Saudiyya ba domin safke farali, kuma yanzu haka maniyya a kasar sun fara shirye-shiryen da suka kamata domin zuwa haji.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshen Azarbaijan cewa; Shugaban musulmin yankin kafkaz ya bayyana cewa; yaduwar murar aladu ba zai hana al'ummar musulmi na kasar Azarbaijan yin tafiya zuwa kasar Saudiyya ba domin safke farali, kuma yanzu haka maniyya a kasar sun fara shirye-shiryen da suka kamata domin zuwa haji. Ya ci gaba da cewa ya gudanar da wata tattaunawa tare da jami'an ma'aikatar kula da harkokin ayyukan haji na kasar Saudiyya, kuma ya jaddada musu cewa matsalar murar aladu ba za ta hana maniyyata daga kasar Azarbaijan zuwa haji ba, kamar yadda ake yadawa kan cewa alhazan kasar ba za su je haji saboda wannan matasala ba babu kamshin gaskiya a cikin hakan.
429374