Bangaren siyasa da zamantakewa; Za a gudanar da taron maulidin Imam Ali (AS) a birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain, wanda cibiyar kula da harkokin ilmi da al'adu ta Iran za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda za a fara daga yau 15 ga watan Tir a babban dakin taro na cibiyar da ke birnin Madrid.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Za a gudanar da taron maulidin Imam Ali (AS) a birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain, wanda cibiyar kula da harkokin ilmi da al'adu ta Iran za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda za a fara daga yau 15 ga watan Tir a babban dakin taro na cibiyar da ke birnin Madrid. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar malamai daga bangarori daban-daban na musulmi da suka hada da malamai da kuma masana da malaman jami'a, inda za su gabatar da laccoci wasu daga cikinsu kuma za su gabatar da makalolin da suka rubuta dangane da wannan maulidi mai daraja.
429595