IQNA

An Gudanar Da Tarukan Maulidin Imam (AS) A Birnin Najaf Mai Alfarm

Bangaren rahoto; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul muminin Ali (AS ) a birnin Najaf mai alfarma, inda baki dayan birnin ya cika da farin ciki da murna, an gudanar da laccoci da kuma wakoki na yabon iyalan gidan manzon Allah SAW a ko'ina cikin birnin mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga gidan talabijin din alfurat cewa; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul muminin Ali (AS ) a birnin Najaf mai alfarma, inda baki dayan birnin ya cika da farin ciki da murna, an gudanar da laccoci da kuma wakoki na yabon iyalan gidan manzon Allah SAW a ko'ina cikin birnin mai alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa taron maulidin Imam Amirul muminin ya samu halartar masoya iyalan gidan manzon Allah daga sassa daban-daban na kasar Iraki da ma kasashen ketare, wadanda suka dauki hanya takanas domin halartar wadannan taruka masu albarka.

430311