IQNA

Alkur'ani Mai Tsarki Yana Warware Matsalolin Zamantakewar Aure

23:50 - July 07, 2009
Lambar Labari: 1799303
Bangaren siyasa da zamantakewa; A cikin addinin musulunci ba a bar wani abu sake ba tare da fayyace bayaninsa ba, kama daga rayuwar ta zamantakewa har zuwa rayuwa ta siyasa da dai dukkanin bangarorin da dan adam ke bukatar Karin haske a kansu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga wani masani bairaniye cewa; A cikin addinin musulunci ba a bar wani abu sake ba tare da fayyace bayaninsa ba, kama daga rayuwar ta zamantakewa har zuwa rayuwa ta siyasa da dai dukkanin bangarorin da dan adam ke bukatar karin haske a kansu. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan masani mai suna Sohan Rahmani ya jadda cewa a duk lokacin da mutum ke bukatar amsa a cikin dukkainin mas'aloli na rayuwarsa ya koma ga kur'ani, idan bai samu amsa kai tsaye ba to ya koma ga kalaman ma'aiki da iyalan gidan zai samu waraka da cikakkiyar amsa.

429593


captcha