IQNA

Imam (AS) Abin Koyi Ne A Cikin Dukkanin Rayuwar Dan Adam

Bangaren rahoto; Imam Amirul muminin Ali (AS) ya kasance abin koyi ne ga dukkanin bangarorin rayuwar biladama, rayuwarsa rayuwa ce mai sauki ba rayuwa ta alfahari da nuna fifiko ba, rayuwarsa rayuwa ce ta imani da tsoron Allah tare da cikakken tsarki da gaskiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daya daga cikin malaman addinin musulunci na kasar Iran Ruhollah Bakiri cewa; Imam Amirul muminin Ali (AS) ya kasance abin koyi ne ga dukkanin bangarorin rayuwar biladama, rayuwarsa rayuwa ce mai sauki ba rayuwa ta alfahari da nuna fifiko ba, rayuwarsa rayuwa ce ta imani da tsoron Allah tare da cikakken tsarki da gaskiya. Malamin ya ci gaba da cewa rayuwar Imam Ali (AS) abin koyi ce ga dukkanin bil adama, domin kuwa ya yi amfani da rayuwarsa wajen aikata kyawan ayyuka, da suka hada kuatata huldarsa da jama'a da kyawawan dabi'u tsakaninsa da mutane baki daya. Rayuwar imam Ali AS ta kasance abin koyi ta fuskacin hakurinsa da ma yadda yakan dauki rayuwar duniya ba a bakin komai ba.

430255