Bangaren rahoto; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul muminin Ali (AS) a kasashen larabawa da ked a mabiya mazhabar shi'a da dama, da suka hada da Bahrain, Kuwait da kuma Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen Khuram abad ya habarta cewa; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul muminin Ali (AS) a kasashen larabawa da ked a mabiya mazhabar shi'a da dama, da suka hada da Bahrain, Kuwait da kuma Labanan. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da tarukan maulidin a kasashen Kuwait da kuma Bahrain da Labanan gami da wasu kasashen wadanada mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ne marassa rinjaye kamar Saudiyya da dai sauransu, inda aka gudanar da wadannan taruka a birnin Madina, haka nan kuma a yankin Katif an gudanar da irin wadannan taruka a masallatai da kuma wuraren gudanar da tarukan addinin musulunci da ke birnin.
430327