IQNA

Malamin Gwamnatin Labanan Ya Gana Da Shugaban Cibiyar Qods

23:24 - July 08, 2009
Lambar Labari: 1799588
Bangaren siyasa da zamantakewa; Malamin gwamnatin Labanan Rashid Qabbani ya gana da shugaban cibiyar Qods ta kasa da kasa Muhammad Akram Adluni a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; Malamin gwamnatin Labanan Rashid Qabbani ya gana da shugaban cibiyar Qods ta kasa da kasa Muhammad Akram Adluni a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanan. Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin ganawar tasu sun tabo muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a birnin Qods, da kuma irin matakan da yahudawan sahyuniya suke dauka na rushe gidajen palastinawa tare da mayar da birnin mallakin yahudawa zalla. Haka nan kuma malaman biyu sun tattauna irin rawar da ya kamata malaman addinin musulunci su taka domin 'yanto Qods daga hannun yahudawan sahyuniya.

430662




captcha