IQNA

An Gudanar Da Maulidin Imam Ali (AS) A birnin Istanbul Na Turkiya

23:24 - July 08, 2009
Lambar Labari: 1799589
Bangaren siyasa da zamantakewa; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul mumini Ali (AS) a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda Iraniyawa mazauna kasar turkiya suka dauki nauyin shirya gudanarwa a babban dakin gabatar da taruka na ofishin jakadancin Iran da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An gudanar da tarukan maulidin Imam Amirul mumini Ali (AS) a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda Iraniyawa mazauna kasar turkiya suka dauki nauyin shirya gudanarwa a babban dakin gabatar da taruka na ofishin jakadancin Iran da ke birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar dukkanin ma'aikatan oishin jakadancin Iran da ke birnin Istanbul da kuma sauran Iraniyawa mazauna birnin, gami da musulmi da dama da na kasar Turkiya musamman ma dai mabiya mazhabar shi'a daga cikinsu. Yayin gudanar da taron an gabatar da jawabai dangane da irin muhimmancin da ke tattare da yin koyi da Imam Amirulmuminin AS a cikin dukkanin bangarori na rayuwa.


430610

captcha