Bangaren siyasa da zamantakewa; Ya zo a cikin ruwayoyi na addini daga bangaren 'yan sunna suna girmama Imam Amirul muminin Ali (AS) da cewa Allah ya karrama fuskarsa, ma'anar hakan kuwa ita ce Allah ya girmama zatin Amirul muminin AS.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa da ke Kermashah cewa; Limamin masallacin juma'a na birnin Runsar Mulla Abdullah Gafur ya gabatar da wani jawabi da acikinsa ya bayyana cewa; Ya zo a cikin ruwayoyi na addini daga bangaren 'yan sunna suna girmama Imam Amirul muminin Ali (AS) da cewa Allah ya karrama fuskarsa, ma'anar hakan kuwa ita ce Allah ya girmama zatin Amirul muminin AS. Ya ci gaba da cewa babban dalilin da ya sanya mabiya mazhabobin sunna suke fadin Allah ya girmama fuskar Imam Ali shi ne, a lokacin zamanin jahiliyya mushrikai suna yin sujada ga gumaka da ke cikin dakin ka'abah, amma Imam Ali bai taba yin sujada ga wani abin halitta ba sai ga Allah subhanahu wa ta'ala.
430652