IQNA

An Fara Baje Kolin Kayyakin Tarihin Masallacin Qods A Labanan

23:23 - July 08, 2009
Lambar Labari: 1799591
Bangaren siyasa da zamantakewa; An bude wani baje kolin kayyakin tarihi dangane da masallacin Qods mai alfarma a sannin palastinawa 'yan gudun hijira da ke yankin Shubraiha a birnin Sur na kasar Labanan, wanda cibiyar raya tarihin musulunci ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; An bude wani baje kolin kayyakin tarihi dangane da masallacin Qods mai alfarma a sannin palastinawa 'yan gudun hijira da ke yankin Shubraiha a birnin Sur na kasar Labanan, wanda cibiyar raya tarihin musulunci ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa a wurin gudanar da wannan baje koli an kawo kayyaki da suke nuna tarihin masallacin Qods mai alfarma, da kuma yadda yahudawan sahyuniya suka shiga cikin yankunan palastinawa tare da mamaye su, da kuma kwace harkokin birnin daga al'ummar muslmi, inda hakan ke nuni da cewa yahudawan sahyuniya na shirin mayar da birnin Qods mallakinsu su kadai.430637









captcha