Bangaren kasa da kasa; Jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a cikin harabar masallacin Qods, bayan da yara 'yan makaranta suka tattaru a cikin masallacin da nufin gudanar da taron gasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga talabijin din palastinu cewa; Jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a cikin harabar masallacin Qods, bayan da yara 'yan makaranta suka tattaru a cikin masallacin da nufin gudanar da taron gasar. Bayanin ya ci gaba da cewa jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kayan sarki sun rufe masallacin a lokacin da aka sanar za a gudanar da gasar, kamar yadda suka kori dukkanin yara 'yan makaranta da suka taru a kusa da masallacin Qods domin halartar gasar.
431061