Bangaren kasa da kasa; Bayan snar da kasha wata musulma 'yar kasar maser da ke zaune a kasar Jamus, saboda dalilai na nuna kyama ga addinin musulunci, an bukaci da mayar da ranar shadarta a matsayin ranar hijabin musulunci ta duniya, kamar yadda wasu daga cikin masana addinin musulunci suka bayar da shawara.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islamonline cewa; Bayan snar da kasha wata musulma 'yar kasar maser da ke zaune a kasar Jamus, saboda dalilai na nuna kyama ga addinin musulunci, an bukaci da mayar da ranar shadarta a matsayin ranar hijabin musulunci ta duniya, kamar yadda wasu daga cikin masana addinin musulunci suka bayar da shawara. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shafi na internet ya kirayi dukkanin mata musulmi a duk inda suke cikin fadin duniya da su gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna rashin amincewa dangane da kisan gillar da aka yi Marwa saboda saka hijabin musulunci a kasar Jamus, wanda ake kallon haka a matsayin wani shiryayyen lamari.
431063