IQNA

An Girmama Wadanda Suka Halarci Gasar Kur'ani A kasar Faransa

23:48 - July 12, 2009
Lambar Labari: 1800962
Bangaren kasa da kasa; An girmama mahardata kur'ani da suka shiga gasar hardar kur'ani a kasar Fransa, an kuma gudanar da bukin girmama su ne a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran was na kasar faransa cewa; An girmama mahardata kur'ani da suka shiga gasar hardar kur'ani a kasar Fransa, an kuma gudanar da bukin girmama su ne a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gasar ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa tsakanain cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da kuma kungiyoyin musulmi na kasar faransa, gami da hadin gwiwa da kwalejin nazari da bincike kan ilimin sanin halayyar dan adam a kasashen turai. Mutane 160 suka shiga cikin gasar da suka hada maza da mata, dukkaninsu kuma musulmi ne mazauna kasar faransa, da suka hada da 'yan asalin kasar da kuma wadanda suka je suna zaune a kasar.

432119





captcha